Ofishin jakadancin Amurka a Hadaddiyar Daular Larabawa ya yi kira ga daukacin al'ummar kasar da su kiyaye matakan tsaro sosai domin kada su jefa rayuwarsu a cikin hadari.
Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da sojojin Yemen da kuma dakarun sa kai na kabilun larabawan kasar suka kai hare-haren mayar da marani kan Hadaddiyar Daular Larabawa da Saudiyya a safiyar yau, sakamakon hare-haren da suke kaddamarwa kan al’ummar kasar Yemen.
Sojojin Yaman sun kai hari kan wurare masu muhimmanci a Dubai da Base Air Base na Al-Zafra da makamai masu linzami a Abu Dhabi a ranar Litinin, 24 ga Fabrairu.
Mohammed al-Bakhiti, mamba a majalisar siyasar Ansarullah ta Yemen a wata hira da tashar Amayadeen ya bayyana cewa, " Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi watsi da shawarar da muka ba ta game da yakin Yemen, kuma a yanzu muna bayar da shawara ga masu zuba jari a UAE da su fice daga kasar.